News
Lokaci Ya Yi Da Za A Daina Daukar Gidajen Rediyon Kano A Matsayin Matattarar Batanci
Shugabannin gidajen rediyo da talabijin a Jihar Kano sun dauki matakin dakile amfani da kafafen yada labarai wajen cin mutunci da tayar da hankali, musamman a cikin shirye-shiryen siyasa.
Matakin na zuwa ne bayan wani taron hadin gwiwa da aka gudanar tsakanin Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Kasa (NBC), Ma’aikatar Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kano, da kuma shugabannin kafafen yada labarai na cikin jihar.
Allah Ya Yi Wa Sakataren NRO, Injiniya Abdulkadir Gude Rasuwa
Taron ya mayar da hankali kan yadda wasu kafafen watsa labarai na Kano ke zama wuraren da ake amfani da su wajen yin zagi da batanci ga ‘yan siyasa, malamai, da sarakuna, wanda hakan ke jawo tashin hankali.
A cikin wannan taro, an bayyana cewa wasu daga jihohin makwabta irin su Yobe, Gombe, Bauchi, Jigawa, da Katsina na amfani da gidajen rediyo da talabijin na Kano wajen zagin shugabanni da sauran masu ruwa da tsaki a cikin al’umma. Bayan haka, sukan bar Kano cikin sauki kamar ba a yi komai ba.
“Wasu daga cikin mutanen daga wadannan jihohi suna zuwa Kano ne kawai domin su rika zagi da bata suna, su tayar da husuma, sannan su tafi gida kamar ba su yi laifi ba,” inji wani bangare na sanarwar bayan taron.
A cikin watanni biyu kacal—Janairu da Fabrairu—an samu rahotanni da suka nuna cewa an karya dokokin watsa shirye-shirye sau 262, wanda mafi yawan su na da nasaba da kalaman batanci da tayar da hankali.
A cikin wannan yanayi, Hukumar ta dauki matakai guda uku masu muhimmanci:
1. Duk wanda zai gabatar da hirar siyasa a gidajen rediyo da talabijin dole ne ya rubuta takardar alkawarin kauce wa zagi da bata suna.
2. Masu gabatar da shirye-shiryen za su guji tambayoyi masu tada husuma ko tunzura ra’ayi.
3. An dakatar da duk wasu shirye-shiryen siyasa kai tsaye har sai an tabbatar da tsaftataccen tsarin watsa labarai a gidajen rediyo da talabijin na jihar.
Masana da shugabannin al’umma sun bayyana cewa matakin ba ya nufin hana ‘yancin fadin albarkacin baki, sai dai yana nufin kare martabar jihar da tabbatar da zaman lafiya.
Tijjani Sarki, wani masani a fannin hulda da jama’a kuma mamba a Human Rights Watch Foundation, ya bayyana cewa: “Mu na da ‘yancin magana, amma fa idan hakan zai cutar da wani ko tayar masa da hankali, to ba daidai ba ne.”
Sarki ya kara da cewa lokaci ya yi da za a daina kallon Kano a matsayin wajen da ake gudanar da duk wani abu na cin mutunci ko batanci, sannan a koma matsayin inda ake kula da martabar jihar da zaman lafiya. “Mu dauki mataki tun yanzu kafin al’amura su kure mana hannu,” inji Sarki.
