Connect with us

News

Falalar Kwana Goma Na Farko Na Zul-Hijjah: Shawarwari Daga Manyan Malamai

Published

on

Ramadan

Yayin da watan Zul-Hijjah ke gabatowa, masana addinin Musulunci na kara jan hankalin al’umma game da falalar kwanaki goma na farko na wannan wata mai albarka, tare da ba da shawarwari kan yadda za a amfana da su cikin ibada da kyawawan ayyuka.

A wata tattaunawa da Aminiya, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Triumph, Kano, Shaikh Lawal Abubakar, ya bayyana cewa wannan lokaci na daga cikin mafiya daraja a cikin dukkan watanni na shekarar. Ya ce, “Wannan kwanaki ne mafi falala, Allah Madaukakin Sarki ya rantsuwa da su a cikin Alkur’ani. Manzon Allah (SAW) ya ce ba wani aiki na alheri da ya fi so ga mutum ya yi cikin shekara kamar yawaitar ibada a cikin wadannan kwanaki.”

Advertisement

Yadda Sanata Barau Ke Tallafa Wa Tsarin Gwamnatin Tinubu Wajen Samar da Abinci A Arewa Maso Yamma

Shaikh Lawal ya yi nuni da abubuwan da ake so Musulmi ya yi a wannan lokaci, ciki har da:

Yawaitar salati, istigfari, hailala da karatun Alkur’ani

Advertisement

Yin nafiloli da azumi, musamman ga wadanda ba za su yi aikin Hajji ba

Sadar da zumunci da bayar da sadaka

Advertisement

Ya kara da cewa, “Ana so Musulmi su yi azumi a cikin kwanakin goma, sai dai wadanda za su tafi Hajji kada su yi azumin ranar Arafah, kuma wadanda ba za su yi ba su daina azumi a ranar Sallah, wato cikon goman watan.”

Mai halin yin Layya

Advertisement

Shaikh Lawal ya kuma shawarci al’umma masu karfin yin layya da su kiyaye kada su yi aski ko yanke faratansu a cikin wannan lokaci, domin bin koyarwar Sunnah.

Sadaka A Kwanaki Goman

Advertisement

Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Shaikh Ibrahim Khalil, ya kara jaddada muhimmancin yawaitar bayar da sadaka a cikin kwanakin. Ya ce, “Sadaka ita ce mafi soyuwa a wannan lokaci, ko ta abinci ko duk wani abu. Bayan haka, ana so a dage wajen azumi, nafiloli, karatun Alkur’ani da zikiri.”

Yi wa Kai Hisabi

Advertisement

Shaikh Ibrahim ya kuma karfafa gwiwar Musulmi da su yi amfani da wannan dama wajen yin nazari da hisabi na rayuwarsu, inda ya ce, “Ya kamata kowa ya yi tambayar kansa abin da ya yi daidai da abin da bai yi daidai ba, domin gyara rayuwa a sabuwar shekara.”

A karshe, malamin ya jaddada muhimmancin yin addu’a musamman a ranar Arafah, inda ya ce babu wani lokaci da Allah Yake amsa addu’o’i kamar wannan rana.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending