Connect with us

News

Yadda Matslar Ruwan Sha Ta Addabi Al’ummar Kauyukan Rogo, Gwamnati Da Wakilai Sun Yi Shiru ‎

Published

on

Kano Na Bukatar Litar Ruwa Miliyan 700 Domin Biyan Bukatun Yau Da Kullum

Al’ummar wasu kauyuka da ke karamar hukumar Rogo a Jihar Kano na ci gaba da fama da matsalar karancin ruwan sha da ya dade yana addabarsu, lamarin da yanzu ya tsananta musamman a wannan lokaci na Zafi

‎Kauyukan da abin ya fi shafa sun hada da Nassarawan Yanoko, Unguwar Cikaji, Unguwar Dan Maliki da Gidan Bili, inda mazauna yankin ke cewa sun shafe sama da shekaru cikin wannan matsala ba tare da samun sauƙi ba.

Advertisement

Yadda Sanata Barau Ke Tallafa Wa Tsarin Gwamnatin Tinubu Wajen Samar da Abinci A Arewa Maso Yamma

‎“Rayuwa ta gagara. Ruwan da muke sha daga koramu ne, kuma ba shi da tsafta. Yana da launin jajawur, amma babu wani zaɓi, shi muka dogara da shi,” in ji wani mazaunin yankin da ya tattauna da Jaridar INDA RANKA.

‎Mazauna yankunan sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da wakilan da suka haɗa da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Rogo da Karaye, Hon. Abdullahi Sani Rogo, da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Rt. Hon. Isma’il Falgore, da su kawo musu agaji cikin gaggawa.

Advertisement

‎Sun zargi wakilan da suka zaɓa da yin shiru da watsi da matsalolin da ke addabar su, lamarin da ke ƙara jefa su cikin wahala.

‎Sai dai jami’in hulɗa da jama’a na karamar hukumar Rogo, Abdu Bako Abdullahi, ya ce shugaban karamar hukumar ya shawarci jama’a da su mika ƙorafe-ƙorafensu ta hannun kansiloli domin a ɗauki mataki.

Advertisement

‎A yanzu haka, al’ummar yankin na ci gaba da roƙon Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya sa baki cikin gaggawa, domin kawo karshen wannan matsala da ke barazana ga lafiyarsu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending