News
Ma’aikatan Hukumar Samar Da Ruwan Sha Sun Janye Yajin Aiki A Kano
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano sun janye yajin aikin da suka shiga tun ranar 26 ga watan Fabrairun 2025, sakamakon rashin sanya su a sabon tsarin mafi karancin albashi na gwamnati.
Shugaban kungiyar kwadago ta hukumar, Kwamared Najib Abdulsalam, ya tabbatar da janye yajin aikin yayin tattaunawa da tashar Dala FM a daren jiya.
Ya bayyana cewa janye yajin aikin ya biyo bayan zaman tattaunawa da suka yi da bangarorin gwamnati da lamarin ya shafa.
Martanin ‘Yan Mazaɓar Tarauni Ga Yarima: “Mu Ba Dawakai Ba Ne Da Za Ka Ba Mu Dawa”
“Daga cikin wadanda muka gana da su akwai Kwamishinan Kasafi da Tsare-Tsare na Kano, shugaban NLC na jihar, da wasu manyan sakatarorin gwamnati da kuma masu ba gwamna shawara,” in ji Kwamared Najib.
Ya kuma umarci dukkan ma’aikatan hukumar da su koma bakin aiki daga gobe, Talata 04 ga watan Maris 2025.
Tun farko dai ma’aikatan sun tsunduma yajin aiki ne bisa rashin fara biyan su sabon mafi karancin albashi, wanda gwamnatin Kano ta ki aiwatarwa tsawon watanni hudu.
Hakan na nufin cewa da janye yajin aikin, ana sa ran sake samun wadataccen ruwan sha a Kano bayan makwannina tsaiko.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
