News
Ma’aikatan Bankuna Na Taimaka Wa ’Yan Damfara Wajen Kai Hari Kan Cibiyoyin Kudi – EFCC
Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana cewa wasu ma’aikatan bankuna na cikin wadanda ke taimaka wa ’yan damfara na yanar gizo wajen kai hare-hare kan cibiyoyin hada-hadar kudi a kasar nan.
Olukoyede ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da ya yi da gidan talabijin na TVC a ranar Lahadi, inda ya ce akalla bankuna guda shida ne aka kai wa hari cikin wani tsari na hadin gwiwa da aka tsara daga sassa daban-daban na duniya.
Yadda Sanata Barau Ke Tallafa Wa Tsarin Gwamnatin Tinubu Wajen Samar da Abinci A Arewa Maso Yamma
A cewarsa, binciken da EFCC ke gudanarwa ya nuna cewa wadannan ma’aikata ne ke bai wa masu damfara damar shiga tsarin kwamfutocin banki, wanda hakan ke ba su ikon kwashe makudan kudade cikin dan kankanin lokaci.
Ya ce: “Mutane na amfani da wasu na’urori da zarar sun hada su da tsarin na cikin gida na banki, tare da taimakon wasu ma’aikatan cikin banki, sai su samu damar sarrafa kudaden daga ko ina suke a duniya. A cikin dakikoki kadan, za su iya kwashe biliyoyin Naira.”
Shugaban EFCC ya bayyana cewa ba sa fitar da dukkan kudaden kai tsaye, sai dai su rarraba su zuwa asusun mutane da dama kafin daga bisani a fitar da su ta hanyar amfani da POS da walat.
Olukoyede ya kara da cewa, “Hukumar ta samu nasarar kwato Naira biliyan 9.7, biliyan 6.7 da kuma biliyan 3.7 daga wasu daga cikin bankunan da aka kai wa hare-haren.”
Ya jaddada cewa ba za a iya samun irin wannan cin zarafin tsarin hada-hadar kudi ba tare da taimakon wasu daga cikin ma’aikatan bankunan ba, wadanda suka fahimci tsarin da ake amfani da shi.
Dangane da dalilin da ya sa EFCC ba ta bayyana lamarin a baya ba, Olukoyede ya ce hakan ya zama dole ne domin hana yaduwar fargaba da kuma dakile yunkurin janyewar kwastomomi daga bankuna, wanda hakan ka iya haifar da tabarbarewar tsarin kudi na kasa.
