Connect with us

News

YOSPIS Ta Bukaci Gwamnatin Kano Ta Ayyana Dokar Ta-baci Kan Kwacen Waya Da Fadan Daba

Published

on

Screenshot 20250704 134721

Wata Kungiyar matasa mai zaman kanta, Youth Society for the Prevention of Infectious Diseases and Social Vices (YOSPIS), ta bukaci Gwamnatin Jihar Kano da ta dauki matakin gaggawa ta hanyar ayyana dokar ta-baci kan matsalolin kwacen waya da fadan ‘yan daba da ke kara yawaita a cikin birnin Kano.

‎Shugabar kungiyar, Zainab Nasir Ahmad, ce ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Jumma,a a Kano, inda ta nuna damuwa kan yadda lamarin ke kara tsananta musamman a tsakanin matasa masu amfani miyagun ƙwayoyi.

Advertisement

‎DSP Barau Da Kaddarar Rayuwa

‎Ta ce, “Abin da ke faruwa yanzu a cikin Kano babban barazana ne ga zaman lafiya da walwalar al’umma. Kwacen waya da kai hari a kan tituna da fadan ‘yan daba sun zama ruwan dare, har ma wasu ke rasa rayukansu.”

‎YOSPIS ta bukaci gwamnati da ta hada kai da hukumomin tsaro da kuma kungiyoyin farar hula wajen kafa wani kwamitin hadin gwiwa da zai fuskanci wannan matsala kai tsaye.

Advertisement

‎Kungiyar ta kuma bukaci a kara tsaurara dokokin hana shaye-shaye da daukar matakin ladabtarwa ga masu aikata laifukan da ke tayar da hankalin jama’a a cikin birni.

‎A cewar kungiyar, matakin ayyana dokar ta-baci zai bai wa hukumomin tsaro damar samun cikakken iko na yaki da masu tada zaune tsaye tare da tabbatar da doka da oda.

Advertisement

‎Al’ummar Kano da dama sun bayyana goyon bayansu ga wannan kiran, suna mai cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta tashi tsaye domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending