News
Ango Ya Maka Amaryarsa A Kotu Kan Zargin Satar Waya A Kano
Wani ango mai suna Usman Ali ya maka amaryarsa Maryam a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Jaba, Jihar Kano, bisa zargin ta da satar masa wayoyin hannu guda uku da darajarsu ta kai kimanin naira 65,000.
A cewar karar da aka shigar a kotun, angon ya bayyana cewa amaryar tasa ta yi amfani da damar kasancewarta a cikin gidan, inda ya zargeta da sace masa wayoyin hannu uku kafin ta gudu daga gidan zuwa wajen iyayenta a Kano.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya nada Ahmed Musa Janar Manaja na Kano Pillars
Sai dai yayin kare kanta a gaban kotu, Maryam ta musanta zargin da ake mata, tana mai cewa ta bar gidan ne domin tserewa daga dukan da mijinta ke yi mata, kuma ta ce ta biya kudin motar dawowa Kano daga Abuja da kudin da ta tara da kanta, ba wai da wani abu mallakar mijin ba.
Bugu da ƙari, angon ya kuma shigar da kawayen amaryar guda uku a gaban kotun, bisa zargin suna hure mata kunne da ƙarfafa mata gwiwar fita daga gidansa ba tare da izini ba.
Alkalin kotun, Ustaz Rabiu Yahaya, ya bayar da belin Maryam, tare da dage shari’ar zuwa ranar 15 ga watan Yulin da muke ciki domin ci gaba da sauraron karar.
AREWA UPDATE ta tattaro cewa dai lamarin ya janyo cece-kuce a tsakanin iyalai da makwabta, inda kowanne bangare ke kokarin kare nashi.
