News
NiMet Ta Gargadi ’Yan Nijeriya Kan Matsalolin Sauyin Yanayi
Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMet) ta bukaci ’yan Nijeriya da su kasance cikin shiri domin sauyin yanayi da kuma matsanancin yanayin da zai iya biyo baya sakamakon sauyin da ke faruwa a duniya.
Daraktan hukumar, Farfesa Charles Anosike, ne ya yi wannan kira a wani taron wayar da kai na kwana ɗaya da aka gudanar a Abuja tare da wakilan kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin farar hula.
Anosike ya ce kafafen yaɗa labarai na da rawar gani wajen isar da muhimman bayanai kan yanayi zuwa ga jama’a. Ya bayyana cewa: “Nasarar ayyukanmu ba ta ta’allaka ne kawai ga daidaiton hasashenmu ba, har ma da yadda bayanan ke isa ga jama’a cikin lokaci da fahimta.”
Ya ce hukumar ta ɗauki matakai daban-daban domin inganta ayyukan sabis na hasashen yanayi da sadarwa, ciki har da horas da ma’aikata da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa da sassa daban-daban domin fuskantar ƙalubalen sauyin yanayi.
A jawabin sa, mai shirya taron, Bonaventure Melah, ya ce taron yana da nufin haɓaka sadarwa da fahimta tsakanin kwararrun NiMet da kafafen yaɗa labarai, domin tabbatar da cewa bayanan yanayi suna isa jama’a cikin sauƙi da fahimta.
Shi ma Darektan Sashen Hasashen Yanayi (DWFS), Farfesa Bincent Weli, ya ce sauyin yanayi na tasiri kai tsaye a rayuwar yau da kullum, don haka yana da muhimmanci mutane su ɗauki matakin kare kansu da dukiyoyinsu.
NiMet na daga cikin hukumomin da ke gaba-gaba wajen bibiyar sauyin yanayi a Najeriya, tare da bayar da rahotanni da hasashe da nufin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
