Connect with us

News

Tsohon Ma’aikacin Radio Kano, Malam Ali Sufi Utai, Ya Rasu Yana Da Sama Da Shekara 100

Published

on

1751808230771

Tsohon ma’aikacin gidan rediyo na Radio Kano, Malam Ali Sufi Utai, ya rasu yana da shekaru sama da 100 a duniya.

Ɗansa kuma ɗan jarida, Auwalu Ali Sufi Utai, ne ya tabbatar da hakan cikin wata hira da ya yi da NIGERIAN TRACKER.

Advertisement

Ya Kamata A Fara Tilasta Wa Matasa Samun Horon Soji A Najeriya – Ihejirika

A cewar Auwalu, mahaifinsa ya rasu ne bayan fama da jinya, inda ya kasance ɗaya daga cikin ma’aikatan da suka sadaukar da rayuwarsu wajen aiki tukuru a gidan rediyon Radio Kano — ɗaya daga cikin tsoffin gidajen rediyo a Najeriya.

Marigayin ya rasu ne kwanaki shida da suka gabata, inda ya bar ’ya’ya da jikoki da tattaba-gida da dama.

Advertisement

An haifi Malam Ali Sufi Utai a garin Utai da ke ƙaramar hukumar Wudil, a jihar Kano, inda ya shahara da rikon gaskiya da sadaukarwa a aikinsa na rediyo.

Ana sa ran za a gudanar da addu’o’i na musamman domin roƙon rahamar Allah a gare shi, tare da jaje ga iyalansa da al’ummar Wudil gaba ɗaya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending