News
“Sanin Kai Shi Ne Matakin Farko Na Ci Gaba” — Turakin Kano
Turakin Kano kuma Hakimin Gwale, Alhaji Mahmud Ado Bayero, ya bukaci al’umma musamman matasa su fara sanin kansu da darajarsu a rayuwa, kafin su nemi sanin wasu abubuwa na waje, domin hakan ne kadai hanyar da za ta ba su damar samun ci gaba mai dorewa.
Bayero ya bayyana haka ne a yayin wani taron ilimi mai taken “Ga Fili Ga Mai Doki” da aka gudanar a Kwalejin Ilimi ta Aminu Kano (AKCOE), da hadin gwiwar Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) da kungiyar daliban Hausa a karkashin jagorancin Kwamared Abubakar Sabo.
Tsohon Ma’aikacin Radio Kano, Malam Ali Sufi Utai, Ya Rasu Yana Da Sama Da Shekara 100
A cewar Turakin Kano, “Sanin kai shi ne ginshikin daraja da mutunci. Idan mutum ya san kansa, zai rika girmama kansa da al’adarsa a ko ina ya tsinci kansa. Dole ne kowane Bahaushe ya rika tafiya da dabi’unsa na gaskiya da mutunci.”
A nasa jawabin, Shugaban Kwalejin, Dakta Ayuba Ahmad Muhammad, ya ce sashen Hausa yana sane da irin aikin da yake yi, kuma zai ci gaba da mara musu baya tare da bayar da duk wata gudunmawa da suka dace da ita a duk lokacin da za su gabatar da wani taro.
Shi kuwa Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya bayyana cewa manufar taron ita ce a bayyana yadda ake tsara waka ta Hausa, da yadda za a rika furta ta da sauti da kuma amfani da ita wajen isar da saƙonni ga al’umma.
Fitaccen mawakin Hausa, Alhaji Babangida Kakadawo, wanda ya gabatar da waka a wajen taron, ya ce wakokinsa tun fil’azal na nufin ilmantarwa, fadakarwa da wa’azantarwa ne.
Shugaban Sashen Hausa na makarantar, Dr Mahe Isah Ahmad, ya ce wannan taro ba na dalibai kadai ba ne, “amma na kowane mai kishin Hausa, musamman ganin cewa wannan shi ne karo na farko da irin wannan taro ke gudana tun kafuwar wannan makaranta.”
