Connect with us

Politics

‎Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa Ya Sauya Sheƙa Zuwa ADC

Published

on

Jam'iyyar ADC

Tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Chief John Odigie Oyegun, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar tare da komawa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), yana mai caccakar gwamnatin APC da gazawa wajen magance matsalolin yunwa da rashin tsaro a ƙasar nan.

Oyegun ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da manema labarai a birnin Benin, yayin da ya karɓi katin zama ɗan jam’iyyar ADC daga shugaban jam’iyyar a jihar Edo, Kennedy Odion.

Advertisement

TikTok Ya Goge Fiye Da Bidiyo Miliyan 3.6 a Najeriya Saboda Saba Ka’idoji

‎Ya ce gwamnatin APC ta gaza cika alkawuran da ta ɗauka, musamman wajen samar da abinci mai araha da tsaro ga al’umma. Ya bayyana cewa, “Halin da al’umma ke ciki a yau, musamman a wasu jihohi kamar Benue, na nuna irin gazawar da ke cikin tsarin mulkin jam’iyyar APC.”

‎Tsohon gwamnan na Edo ya ce ya ɗauki lokaci mai tsawo yana nazari da tuntubar masu ruwa da tsaki kafin yanke shawarar sauya sheƙa. Ya bayyana ADC a matsayin jam’iyyar da ke da hangen nesa da cikakken shiri na ceto ƙasar daga matsin rayuwa.

Advertisement

‎“Ba mu ɗauki wannan mataki da wasa ba. Mun tantance jam’iyyu da dama kafin mu fahimci cewa ADC ce za ta iya fitar da Najeriya daga wannan hali da ake ciki,” in ji Oyegun.

‎Ya ƙaryata rade-radin da ke cewa haɗin gwiwar siyasa da ADC ke jagoranta na da nufin kawo cikas ga gwamnatin APC, yana mai cewa waɗanda ke yaɗa irin waɗannan jita-jita na ƙoƙarin karkatar da hankalin jama’a daga ainihin batun gyara ƙasa.

Advertisement

‎Oyegun ya ce a ‘yan makonnin da suka gabata, ADC ta karɓi sabbin mambobi daga sassa daban-daban na siyasa, ciki har da tsofaffin ‘yan PDP da APC, masana, da sabbin matasa masu kishin ƙasa.

‎A cewarsa, “Abin da muke buƙata yanzu shi ne sauyi na gaskiya wanda zai dawo da martabar Najeriya da walwalar jama’a. Kuma wannan sauyi ba zai samu ba sai da sabuwar jam’iyya mai akida da tsari.”

Advertisement

‎Oyegun ya jaddada cewa yana da yakinin ADC za ta zama madaidaiciyar mafita ga ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta a yau.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending