Connect with us

News

Yansanda Sun Gano Gawar Dan Jarida Mai Daukar Hoto Da Makwabcinsa Ya Hallaka  

Published

on

Ayo 1

Rundunar Ƴansandan jihar Kogi ta tabbatar da gano gawar wani ɗan jarida mai ɗaukar hoto, Ayo Aiyepeku, wanda ake zargi makwabcinsa, Oluwapelumi Adebayo, ya yi ajalinsai.

Daily Trust ta rawaito cewa kakakin rundunar, SP Williams Aya, ya ce an gano gawar ne da yammacin Lahadi a kusa da ofishin WAEC, unguwar Crusher, Zone 8, Lokoja, bayan kwanaki da ɓacewarsa.

Advertisement

A cewar SP Aya, an kashe Ayo ne a daren Talata, 22 ga watan Yuli, a wani ofis da ke kusa da GRA/Gidan Gwamnati a Lokoja, kuma tuni aka kai gawar asibitin gwamnatin jihar.

Adadin Mutanen Da Suka Rasa Rayukansu Sanadiyyar Ambaliyar Ruwa A  Adamawa Ya Karu Zuwa 23

Dangin mamacin da abokansa sun roƙi gwamnati da hukumomin tsaro su tabbatar da adalci, inda ɗan uwansa, Timothy Aiyepeku, ya yi kira da a gano hakikanin abin da ya faru.

Advertisement

Rahotanni sun nuna cewa wasu mazauna yankin ne suka gano gawar a cikin daji, bayan sun ji wari da ke tashi daga wajen

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending