Connect with us

News

An Kama Basarake Kan Zargin Cin Zarafin ’Yar Shekara 12 A Gombe

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wani basarake, Mohammed Tukur mai shekaru 55, a kauyen Sabon Gari da ke yankin Zambuk na Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe.

‎Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

‎Gwamnatin Kano Ta Bayar Da Kwangilar Hanyoyi 17 Akan Sama Da  Naira Biliyan 40

 

‎Ya ce abin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar 9 ga Agusta, 2025, lokacin da ake zargin ya yaudari yarinyar wadda ya kaita wani wuri da babu idon jama’a ya aikata ta’asar.

‎Bayan samun rahoton faruwar lamarin ne, jami’an ’yan sanda daga ofishin Zambuk suka hanzarta zuwa wurin, sannan suka mika yarinyar zuwa Asibitin Zambuk domin duba lafiyarta.

‎Nan take dai rundunar ta cika hannu da wanda ake zargin, kuma a halin yanzu yana tsare a hannun ’yan sanda, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

Advertisement

 

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending