News
Majalisar Dattawa Na Duba Yiwuwar Baiwa Jami’an Tsaro Damar Kada Kuri’a Kafin Ranar Zaɓe
Majalisar Dattawan Najeriya ta shiga tattaunawa da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, kan yiwuwar yi wa kundin tsarin mulki gyara domin baiwa jami’an tsaro damar kada kuri’a kafin ranar babban zaɓe.
Sanata Abdulaziz Yaradua, wanda ya jagoranci tawagar, ya gabatar wa Egbetokun da ƙudirin dokar domin ya yi nazari tare da hukumomin sa, kafin majalisa ta yi nazari na ƙarshe da kuma amincewa.
An Kama Basarake Kan Zargin Cin Zarafin ’Yar Shekara 12 A Gombe
A halin yanzu, Najeriya na cikin jerin ƙasashen da jami’an tsaro, ma’aikatan lafiya da ‘yan jaridu ba su da damar yin zabe saboda yanayin aikin su, tare da rashin wani tsari na musamman daga gwamnati.
Egbetokun ya yaba wa Sanata Yaradua da sauran ‘yan majalisa bisa yunƙurin ganin an baiwa jami’an tsaro damar amfani da haƙƙin su na zaɓe.
A ƙasashen da suka ci gaba, ana baiwa jami’an tsaro, ma’aikatan lafiya da ‘yan jaridu damar kada kuri’a kwanaki kafin ranar zaɓe domin ba su damar ci gaba da gudanar da aikinsu ba tare da tangarda ba.
