News
Gwamnatin Tarayya Na Shirin Kara Albashin Masu Rike Da Mukaman Siyasa
Hukumar Rarraba Kuɗaɗe da Albashi (RMAFC) ta bayyana cewa tana shirin sake duba albashin shugabannin siyasa a Najeriya, tana mai cewa tsarin da ake amfani da shi yanzu ya tsufa kuma bai dace da alhakin da ke kansu ba.
Shugaban hukumar, Mohammed Shehu, ya bayyana hakan a taron manema labarai a Abuja ranar Litinin.
Gwamnatin Legas Ta Kwace Baburan Okada 668 A Cikin Mako Guda.
Ya ce Shugaba Bola Tinubu na karɓar N1.5m a wata, yayin da ministoci ke samun ƙasa da N1m adadi da bai canza ba tun shekarar 2008.
Shehu ya ce tsarin biyan ba ya adalci idan aka kwatanta da nauyin aiki, inda ya nuna cewa shugabannin hukumomi kamar Gwamnan CBN da manyan Daraktoci suna karɓar kuɗi fiye da albashin ministoci da ma shugaban ƙasa.
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su goyi bayan hukumar wajen tsara “albashi mai ma’ana” ga masu rike da mukaman siyasa, shari’a da majalisa.
Sai dai Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta ƙi amincewa da shirin, tana mai cewa hakan bai dace ba a daidai lokacin da talauci da rashin daidaito ke ƙaruwa, tare da abubuwan alfarma da aka ɓoye da ke ƙara yawan kuɗaɗen da ‘yan siyasa ke samu.
NLC ta ce maimakon haka, ya kamata gwamnati ta mai da hankali wajen ƙara albashin ma’aikata da rage tsadar rayuwa.
Shugaban RMAFC ya kuma yi bayanin cewa hukumar ba ta da ikon tsara mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan gwamnati, sai dai albashin ‘yan siyasa, na shari’a da na majalisa ne kawai.
Ya ƙara da cewa hukumar ta fara aiki kan sabon tsarin rabon kuɗaɗe a Najeriya wanda bai sauya ba tun 1992.
A tsarin da ake amfani da shi yanzu, gwamnatin tarayya na karɓar kashi 52.68 cikin 100 na kuɗaɗen da ake tarawa, jihohi 26.72 cikin 100, sannan kananan hukumomi 20.60 cikin 100.
Shehu ya ce dole a sake duba tsarin don ya dace da halin tattalin arzikin yau, ya ƙarfafa tsarin dimokuradiyyar kuɗi, tare da bai wa jihohi damar zama masu dogaro da kansu.
