News
Za A Fara Daure Mazan Da Ba Sa Zuwa Sallar Juma’a A Malaysia
Gwamnatin jihar Terengganu ta ƙasar Malaysia ta sanar da sabuwar doka da za ta fara hukunta duk wani Musulmi mazaunin jihar da ya ki halartar sallar Juma’a ba tare da uzuri ba.
A ƙarƙashin dokar, wanda ya tsallake sallar Juma’a zai iya fuskantar zaman kurkuku har na tsawon shekaru biyu ko kuma tarar Ringgit 3,000 (kimanin Naira miliyan ɗaya), ko ma a hukunta shi da duka biyun.
NiMet Ta Yi Hasashen Samun Ruwan Sama Da Iska Na Tsawon Kwana Uku A Najeriya
Ƙaramin Ministan Shari’a na jihar, Muhammad Khalil Abdul Hadi, ne ya bayyana hakan a jawabin da ya gabatar a farkon mako, yana mai cewa:
“Wannan mataki ya zama dole saboda sallar Juma’a ba wai alama ce ta addini kawai ba, har ila yau tana nuna biyayya da haɗin kai a tsakanin Musulmi.”
A baya dai, hukunci ya tsaya ne a kan wanda ya tsallake sallar Juma’a uku a jere, wanda zai iya fuskantar zaman kurkuku na watanni shida ko tarar Ringgit 1,000 (kimanin Naira dubu ɗari huɗu).
A watan Nuwamba na bara, jihar Johor ta bayyana shirin tabbatar da cewa dukkan mazan Musulmi suna halartar sallar Juma’a. Sai dai a watan Fabrairu 2024, kotun koli ta kasar ta yi fatali da wasu dokokin Shari’a na jihohi da ta ce sun sabawa kundin tsarin mulki.
Malaysia na da tsarin shari’a biyu: dokar farar hula ga kowa da kowa, sannan kuma dokokin Shari’a ga Musulmi da ke wakiltar kusan kashi biyu bisa uku na al’ummar kasar data haura mutane miliyan 34.
