News
Rashin Adalci Ne A Sanya Juma’a A Matsayin Ranar Aiki Ga Musulmi A Najeriya —Reno Omokri
Tsohon mai ba wa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan shawara, Reno Omokri, ya bukaci gwamnati ta sake nazarin tsarin ranakun aiki a Najeriya domin bai wa Musulmi damar gudanar da sallar Juma’a ba tare da cikas ba, yana mai bayyana tsarin da ake amfani da shi yanzu a matsayin rashin adalci.
Omokri ya bayyana hakan ne a wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a, inda ya ce kafin zuwan Turawan mulkin mallaka, Juma’a na kasancewa rana ta hutu ga Musulmi.
Yadda Manoma Ke Fuskantar Gagarumin Ƙalubale A Lokacin Damuna A Najeriya
Ya ce bai dace a bar Lahadi a matsayin ranar hutu ga Kiristoci yayin da ake tilasta wa Musulmi yin aiki a ranar Juma’a ba duk da muhimmancin ranar ga addininsu.
“Ina ganin bai yi wa al’ummar Musulmi adalci ba mu kasance da Juma’a a matsayin ranar aiki a Najeriya. A asali, kafin mulkin mallaka, ba haka abin yake ba,” in ji Omokri.
Ya ba da shawarar cewa gwamnati za ta iya sauya tsarin lokutan aiki domin bai wa Musulmi damar yin sallar Juma’a cikin walwala. A cewarsa, ofisoshi za su iya rufewa tun da wuri a ranar Juma’a, yayin da za a ƙara awannin aiki daga Litinin zuwa Alhamis.
“Maimakon mu fara aiki 8:00 ko 9:00 na safe, za mu iya fara aiki tun 7:30 daga Litinin zuwa Alhamis. A ranar Juma’a kuma mu rufe ofisoshi da misalin ƙarfe 12 na rana,” in ji shi.
Omokri ya jaddada cewa wannan tsari ba zai rage yawan aiki ko habakar tattalin arzikin ƙasa ba, domin za a cike awannin da za a rage a ranar Juma’a daga Litinin zuwa Alhamis.
“Wannan sauyin ba zai shafi ingancin aiki ko ci gaban tattalin arzikin ƙasar ba. Zai kuma bai wa Musulmi damar gudanar da sallar Juma’a cikin natsuwa,” in ji shi.
Ya ce matakin zai taimaka wajen samar da daidaito tsakanin buƙatun addini da tsarin aiki a Najeriya, tare da tabbatar da adalci ga al’ummar Musulmi da Kiristoci.
