Connect with us

News

’Yan Fashi Sun Kwashi Kayan Tarihi Masu Tsadar Gaske A Gidan Tarihi Na Paris Cikin Mintuna Hudu

Published

on

A cikin mintuna hudu kacal, wani gungun ’yan fashi sun kutsa Gidan Tarihi na Musée du Louvre da ke tsakiyar birnin Paris, inda suka yi awon gaba da kayan tarihi da na kwalliya masu tsadar gaske.

Lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi, da misalin ƙarfe uku na asuba agogon Faransa. Rahotanni sun bayyana cewa ’yan fashin sun shiga cikin ginin ta wata ƙofa ta gefe, suka kwashe wasu daga cikin muhimman kayayyakin fasaha da kayan ado masu daraja, kafin su tsere da babura cikin sauri.

Advertisement

‎Ƴansanda Sun Kama Wani Dattijo Mai Shekara 63, Bisa Zargin Satar Babur A Neja.

Hukumar kula da gidan tarihin ta Louvre ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da sanar da cewa an rufe gidan tarihin na ɗan lokaci saboda halin gaggawa da aka tsinci kai a ciki.

Kakakin rundunar ’yan sandan Paris ya ce an kaddamar da bincike mai zurfi domin gano wadanda suka aikata wannan mummunan laifi, yayin da ake ci gaba da neman su a duk fadin kasar Faransa.

Advertisement

Gidan Tarihi na Louvre na daga cikin wuraren tarihi mafi shahara a duniya, kuma yana jan hankalin miliyoyin baƙi daga sassa daban-daban na duniya. Daga cikin abubuwan da suka fi jan hankali a cikinsa har da zanen Mona Lisa na Leonardo da Vinci, wanda ke ɗaya daga cikin kayan tarihi mafi daraja a duniya.

 

Advertisement

 

DW

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending