Sports
Wasan farko da ‘yar kwallo mai sa hijabi ta buga a Gasar Cin Kofin Duniya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
An kafa tarihi a Gasar Kwallon Kafar Mata ta Duniya ta FIFA a karon farko bayan da Nouhaila Benzina, ‘yar wasa ta farko sanye da hijabi, ta buga kwallo a tawagar kasar Maroko mai suna “The Atlas Lionesses.”
Sannan kuma wasan ne karon farko da wata tawagar matan Larabawa daga yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka take fafatawa.
Duk da cewa Jamus ta sha Maroko 6-0 a wasan da aka yi ranar Litinin a Filin Wasa na Melbourne, masoya kwallon kafa daga duniyar Larabawa na fatan tawagar za ta yunkuro a wasanta na gaba.
Benzina, mai shekara 25, wacce take kuma buga wa tawagar Rundunar Sojin Maroko FAR, ta fara wasa a tawagar kasar ne a shekarar 2018.
Gabanin nan, ‘yar wasan bayan ta nuna bajintarta a yayin da take wasa a tawagar ‘yan kasa da shekara 20 ta Maroko a shekarar 2017.
Kasancewarta a filin wasa ya ja hankali sosai saboda batun ba da damar sanya hijabi a yayin wasa.
Nouhaila ta zama wata abar misali ta jajircewa da saka himma ga mata Musulmai da suka shafe shekaru suna neman a daina kyamar Musulunci musamman haramcin da FIFA ta saka na sanya hijabi.
