Sports
El-Classico:Real Madrid Da Barcelona Za Su Barje Gumi yau.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Kungiyoyin kwallon kafa biyu da suka shahara a fagen kwallon kafa ta duniya Real Madrid da Barcelona za su fafata a daren yau.
Sun shirya fafatawa yau ranar 29 ga watan 7 2023 a wani wasan sada zumunta, yayin da ake shirye-shiryen tunkarar sabuwar gasar kwallon kafa ta badi.
Niger: Hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 473 a cikin watanni 6 – FRSC
Fafatawar wadda ake wa lakabi da El-Classico ta kasance wasa mafi zafi a wasannin kungiyoyin kwallon kafa a duniya.
Wasan zai zamo El-Classico na farko da manyan ‘yan wasa da suka hada da Ilkay Gundogan, Jude Bellingham da kuma matashin dan wasa Arder Guler za su fara bugawa.
Advertisements
