News
’Yan Bindiga Sun Sace Shanu Sama Da 60 A Tsanyawa, Kano
Wasu ’yan bindiga masu babura sun kutsa cikin garin Yan Cibi Tsohon Gari a karamar hukumar Tsanyawa, jihar Kano, inda suka sace shanu sama da 60 a daren Asabar.
Wani mazaunin garin da ya bukaci a boye sunansa ya shaida wa Arewa Radio cewa, mazauna da dama sun tsere daga gidajensu saboda tsoro. Ya kara da cewa, ‘yan bindigar sun yi garkuwa da wasu mata, amma daga baya sun sake su bayan sojoji suka isa wurin domin bayar da taimako.
Kungiyar Iyayen Ɗaliban MAAUN Ta Nemi Afuwa Kan Abin Da Ya Faru A Cikin Dakin Jarabawa
Wasu daga cikin mazaunan garin sun ce sun fara shirin barin garin gaba daya saboda tsananin hare-haren.
Garin Yan Cibi Tsohon Gari, dake kan iyaka da jihar Katsina, yana daga cikin yankunan da aka fi samun hare-haren ’yan bindiga a jihar Kano.
Kawo yanzu, hukumomin tsaro ba su fitar da martani kan lamarin ba.
