Connect with us

News

Najeriya Na Rasa Yara 850,000 Duk Shekara Sakamakon Cututtukan Da Za A Iya Magance Su 

Published

on

Zazzabin Lassa Cutar ta yi Ajalin Mutum 118 A Cikin Watanni Uku

Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Muhammad Pate, ya ce Najeriya na fuskantar gagarumar matsala ta mace-macen yara ƙanana, inda kusan yara 850,000 ke mutuwa a duk shekara sakamakon cututtukan da ake iya magance su cikin sauƙi kamar numoniya, cutar gudawa da sauran matsalolin da suka shafi kiwon lafiya.

Pate ya bayyana haka ne a Abuja yayin bikin Ranar Yaki da Numoniya da Haihuwar Jarirai Bakwaini ta Duniya ta 2025, inda ma’aikatar ta ƙaddamar da wasu muhimman tsare-tsare biyu da suka haɗa da Shirin Ceton Yara da kuma Ka’idojin Magance Matsalolin Haihuwa.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Yaki Da Cin Ganda A Najeriya

Daraktan Inganta Harkokin Lafiya, John Urakpa, wanda ya wakilci ministan a taron, ya ce an samu raguwar mace-macen yara ƙasa da shekara biyar a ƙasar, bisa ga kididdigar NDHS.

A shekarar 2000, yara 200 cikin 1,000 ne ke mutuwa kafin su kai shekara biyar. Amma zuwa 2023, adadin ya sauka zuwa 110 cikin 1,000 — raguwar kusan kashi 45% cikin shekaru 23.

Advertisement

Sai dai ya ce duk da wannan ci gaban, Najeriya na ci gaba da rasa yara 850,000 a duk shekara, abin da ya nuna cewa ƙasar na da tazarar da ta kamata ta taka kafin ta cimma burin SDGs na rage mace-macen yara zuwa 25 cikin 1,000 nan da 2030.

A faɗar ministan, kusan jarirai 280,000 na mutuwa cikin kwanaki 28 da haihuwa saboda matsalolin da suka haɗa da haihuwa kafin lokaci.

Advertisement

Ya ƙara da cewa yara 162,000 na mutuwa duk shekara saboda numoniya, wadda ke daga cikin manyan cututtukan da ke kashe yara ƙanana a duniya.

A cewar Pate, a duniya ana samun miliyan 100 na sabbin kamuwa da numoniya a duk shekara, inda akalla 808,000 ke mutuwa – mafi yawan su a yankin Afirka kudu da Sahara.

Advertisement

Ya ce Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashe 15 da ke da kashi mafi tsoka na mace-macen da numoniya ke janyo wa.

Pate ya bayyana numoniya a matsayin “makashin yara da aka manta da shi”, yana mai cewa an mai da hankali sosai kan cututtuka irin su Maleriya, Foliyo, HIV da Tarin Fuka, amma numoniya ta ci gaba da zama barazana ba tare da irin kulawar da ya dace ba.

Advertisement

Ministan ya yaba da haɗin gwiwar da ake yi da kungiyoyi kamar Every Breath Counts Coalition da Kungiyar Likitocin Yara ta Najeriya, wadda ta taimaka wajen inganta kwarewar ma’aikatan lafiya a cibiyoyin kula da numoniya.

A cewarsa, wannan ya taimaka wajen rage mace-macen yara ƙasa da shekara biyar daga 132 cikin 1,000 a 2018 zuwa 110 cikin 1,000 a 2024.

Advertisement

Sai dai ya ce a fannin jarirai, raguwar mace-mace bai yi wani gagarumin tasiri ba cikin shekaru 35, inda adadin ya tsaya a kusa da 41 cikin 1,000 tun daga 1990 zuwa 2024.

 

Advertisement

 

PREMIUM TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending