News
“Iyalan Dalibin Da Aka Kashe A Kaduna Sun Kalubalanci Gwamnati Kan Sakin Wanda Ake Zargi”
Iyalan marigayi Ahmed Musa, dalibin da aka kashe a Government Technical College Malali, Kaduna, a ranar 16 ga Fabrairu 2025, sun bayyana rashin jin daɗinsu kan yadda aka saki wanda ake zargi da kisan.
A wata sanarwa da mahaifin marigayin, Comrade Musa Mohammed (Moonlight) ya fitar, iyalan sun ce sakin wanda ake zargi ya kawo tsaiko wajen samun adalci.
Allah Ya Yi Wa Sheikh Dahiru Bauchi Rasuwa Yana Da Shekara 101 A Duniya
Iyalan na ganin gwamnatin jihar ta yi watsi da su, lamarin da suka ce ya jefa su cikin jin an yi musu rikon sakainar kashi wajen samun Adalci.
“Muna bukatar shari’a mai gaskiya kuma a gudanar da ita ba tare da katsalandan na siyasa ba,” in ji iyalan.
Sun ce za su kai ƙara Babbar Kotun Tarayya domin neman hakkinsu tare da neman diyya ta N560,300,000, bisa cewar sakin wanda ake zargi ya cutar da su matuƙa.
Haka kuma, iyalan sun ce za su shirya zanga-zangar lumana a fadin Kaduna domin wayar da kan jama’a da kuma neman goyon baya wajen ganin an kai ga samun adalci ga marigayi Ahmed Musa.
Iyalan sun nemi jama’a da ƙungiyoyin kare hakkin bil’adama da su mara musu baya a wannan yunkuri.
