Connect with us

News

Hon. Da’u Aliyu Abubakar Ya Zama Jakadan Hukumar Kashe Gobara A Kano

Published

on

IMG 20251127 WA0004

Hukumar kashe gobara ta ƙasa reshen jihar Kano, tare da haɗin gwiwar kasuwar Wayoyi ta Farm Center, ta nada Hon. Da’u Aliyu Abubakar (Kogunan Ƙasar Hausa) a matsayin Jakada na hukumar.

An gudanar da nada shi a ɗakin taro na hukumar dake kasuwar Wayoyi ta Farm Center, a wani mataki na wayar da kan jama’a kan dabarun kare kai daga gobara da sauran haɗurran da ka iya janyo asarar dukiya ko rayuka.

Advertisement

“Iyalan Dalibin Da Aka Kashe A Kaduna Sun Kalubalanci Gwamnati Kan Sakin Wanda Ake Zargi”

Hon. Da’u Aliyu ya bayyana matuƙar farin cikinsa da samun wannan mukami, inda ya yi kira ga al’umma, musamman masu hannu da shuni da kamfanoni masu zaman kansu, da su tallafawa wayar da kan jama’a kan yadda za su kare kansu daga gobara. Ya jaddada muhimmancin ɗaukar matakan tsaro musamman a wannan lokaci na sanyi da samar da kayayyakin kariya.

A karshe, ya gode wa hukumar kashe gobara ta ƙasa reshen Kano bisa jajircewarsu wajen wayar da kan jama’a domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending