Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Sake Yin Garkuwa Da Manoma 24 A Neja

Published

on

Yan bindiga sun sake yin garkuwa da manoma 24, a gonar shinkafa da ke karamar hukumar Shiroro a Jihar Neja

Mazauna yankin sun ce maharan sun afka gonar ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana, lokacin da manoman ke cikin aikin girbin amfanin gona na bana.

Advertisement

Yan Bindiga Sun Sake Yin Garkuwa Da Manoma 24 A Neja

Duk da cewa ofishin soji na Erena na da nisan kusan kilomita biyar kacal daga yankin, ’yan bindigar sun tsere cikin sauƙi tare da mutanen da suka yi garkuwa da su, kafin jami’an tsaro su isa wurin.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ceto waɗanda aka akayi garkuwa da su. A ranar da abin ya faru, wasu ’yan bindiga daban sun kutsa Kauyen Kakuru.

Advertisement

 

ArewaRadio

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending