News
Shekaru 45: Rikicin Maitatsine Ya Bar Baya Da Kura
Shekara arba’in da biyar da suka gabata, rikicin Maitatsine ya girgiza Jihar Kano, inda ya sauya birnin daga cibiyar kasuwanci zuwa wani launi mara daɗin faɗe.
Rikicin ya ɓarke ne a Disambar 1980, bayan da ’yan sanda suka je filin wasa na Shahuci, kusa da Masallacin Juma’a na Kano, domin cafke mabiyan wani mai tsattsauran ra’ayi, Muhammadu Marwa, wanda aka fi sani da Maitatsine, bisa zargin wa’azi ba tare da izini ba.
Rahotannin wancan lokaci sun nuna cewa jami’an tsaron sun fada tarkon kwanton ɓauna, inda mabiyan Maitatsine suka kai musu hari da makamai na gargajiya.
An ƙona motocin ’yan sanda, hanyoyi suka toshe, kuma lamarin ya rikide zuwa mummunan rikici.
Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta ruwaito cewa motocin ’yan sanda tara sun ƙone, jami’an tsaro huɗu sun mutu, yayin da asibitoci suka gagara aiki sakamakon rashin tsaro.
Rahotanni sun kiyasta mutuwar kusan mutane 100 a daren farko kaɗai.
Rikicin ya ɗauki kwanaki 11, inda rahotanni daban-daban suka nuna cewa sama da mutane 4,000 ne suka rasa rayukansu kuma yawancinsu fararen hula ne.
Daya daga cikin waɗanda suka tsira daga rikicin, Hajiya Aishatu Adamu (Atine), ta ce a farkon zuwan Maitatsine unguwar Koki, ba a ɗauke shi a matsayin barazana ba.
“Muna ganin malami ne. Yana da makaranta, muna tsammanin yana koyar da Karatun addini yake yi,” in ji ta.
Ta ce daga bisani mabiyansa suka fara hana jama’a zirga-zirga, tare da tsangwama ga mazauna yankin.
Matakan gargadi da aka yi biris da su
Wani dattijo a Koki, Baba Habibu, ya ce tun kafin rikicin, mazauna yankin sun rika lura da shige-da-ficen mutane masu ɗauke da makamai zuwa gidan Maitatsine
Ya ce sun kai ƙorafe-ƙorafe ga hukumomi, amma maimakon ɗaukar mataki, wasu daga cikin masu ƙorafin aka kama.
“Mun kai rahoto, amma mu aka tsare,” in ji shi.
Baba Habibu ya kuma ce daga baya ya fahimci cewa rikicin ba kwatsam ba ne, domin mabiyan Maitatsine na da tsari tun kafin barkewar tashin hankalin.
Tarihi ya nuna cewa Sarkin Kano na wancan lokaci, Muhammadu Sanusi I, ya taba korar Maitatsine daga Kano a shekarun 1950, sakamakon korafe-korafe kan tsattsauran ra’ayinsa.
Sai dai bayan sauye-sauyen siyasa, Maitatsine ya dawo Kano, inda ya sake tara mabiya a yankin Koki.
Masana tarihi na ganin cewa rashin tsayuwar doka da tsari a wancan lokaci ya taimaka wajen sake samun karfinsa.
Lokacin da rikicin ya ƙara tsananta
Yayin da rikicin ya tsawaita, unguwanni da dama sun zama wuraren da ba a iya shiga.
Hajiya Atine ta ce a wannan lokaci ta rasa mijinta, tare da fuskantar tsarewa da azaba a hannun mabiyan Maitatsine.
Ta ce bayan shigar sojoji cikin lamarin, an samu damar ceto mata da yara, inda aka kai su sansanin wucin gadi kusa da kasuwar Kurmi.
Wani masanin tsaro, Dr. Yahuza Getso, ya ce kashe Maitatsine bai kawo ƙarshen matsalar tsattsauran ra’ayi ba.
“An kashe Maitatsine, amma an bar tunaninsa. Abin da Boko Haram da ISWAP ke yi a yau yana da kamanceceniya da abin da ya faru a Kano a wancan lokaci,” in ji shi.
Ya ce rashin ɗaukar mataki kan yaduwar makamai da talauci ya taimaka wajen sake bullar irin waɗannan ƙungiyoyi a Arewacin Najeriya.
Duk da cewa Kanawa sun koma rayuwarsu ta yau da kullum, Sun tsira daga rikicin Maitatsine amma haryan zu a jihar ana rayuwa da raɗaɗin abin da ya faru.
“Lokaci ya wuce, amma abin da muka gani ba zai taɓa fita daga zuciyarmu ba,” in ji Hajiya Atine.
