Connect with us

News

ZARGIN YUNƘURIN KIFAR DA GWAMNATI: Falana Ya Bukaci Sojoji Su Ba ’Yan Najeriya Haƙuri

Published

on

Falana

Fitaccen lauya mai kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana (SAN), ya caccaki Rundunar Sojin Najeriya kan yadda ta tafiyar da zargin yunƙurin juyin mulki da aka danganta da wasu jami’anta.

Falana ya ce rundunar ya kamata ta ba ’yan Najeriya haƙuri, saboda yadda aka rikita lamarin tun farko.

Advertisement

Wutar Lantarki Ta Sake Lalacewa Karo Na Biyu A Shekarar 2026

A watan Satumba 2025, Hukumar Leken Asiri (DIA) ta kama manyan jami’an soji 16, ciki har da Birgediya Janar, Kanal, Laftanar Kanar da Manjoji, bisa zargin shirya kifar da gwamnati. Sai dai kwanan nan, Rundunar Sojin Najeriya (AFN) ta sanar da kammala bincike, inda ta ce wasu daga cikin jami’an za su fuskanci kotunan soja kan laifukan rashin ladabi da saba dokokin aiki.

Advertisement

Falana ya bayyana hakan ne a ranar Talata a shirin The Morning Brief na Channels TV, inda ya ce rundunar ta ruɗi jama’a tun farko, saboda a baya ta musanta rahotannin yunƙurin juyin mulki gaba ɗaya.

“Abin da ya kamata rundunar soji ta yi jiya shi ne ta ba ’yan Najeriya haƙuri. Dole ne masu riƙe da madafun iko su fara girmama jama’a,” in ji Falana.

Advertisement

Ya ce janye matsaya ba tare da neman afuwa ba abin Allah wadai ne, musamman ganin cewa a baya rundunar ta musanta yunƙurin juyin mulki gaba ɗaya.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending