News
Wutar Lantarki Ta Sake Lalacewa Karo Na Biyu A Shekarar 2026
Rumbun wutar lantarki na ƙasar Nijeriya ya sake fāɗuwa a karo na biyu cikin shekarar 2026, lamarin da ya haifar da ɗaukewar wuta a sassa daban-daban na ƙasar a ranar Talata.
Kamar yadda tashar talabijin ta Channels ta ruwaito, bayanai sun nuna cewa, zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto, babu ko megawatt ɗaya na wutar lantarki da ake samarwa domin rarrabawa ga kamfanonin rarraba wuta 11 na ƙasar.
SIYASAR KANO: Kwamishinoni 5 Da Hadiman Gwamnati 10 Sun Yi Murabus
Wannan na faruwa ne makonni kaɗan bayan fāɗuwar rumbun wutar a karo na farko a bana, wadda ta auku a ranar Juma’a da ta gabata. Haka kuma, an samu irin wannan matsala a ranar 29 ga Disamba, 2025.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (TCN) ba ta bayyana dalilan da suka haddasa wannan matsala ba.
