News
SIYASAR KANO: Kwamishinoni 5 Da Hadiman Gwamnati 10 Sun Yi Murabus
Akalla kwamishinoni biyar da kuma hadiman gwamnati goma sun yi murabus daga muƙamansu, tare da ayyana biyayya da goyon baya ga jagoran Kwankwasiyya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso.
Rahotanni sun nuna cewa murabus ɗin ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar tashin hankalin siyasa da rabuwar kai tsakanin Injiniya Kwankwaso da Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf.
Shugaban Ghana Ya Kara Wa Dakarun Soji Albashi
Kafar yaɗa labarai ta Arewa Updates ta bayyana cewa ta tattaro wannan adadi zuwa safiyar Talata, 27 ga Janairu, 2026, inda ta ce jerin jami’an da suka ajiye muƙamansu na iya ƙaruwa.
Daga cikin kwamishinonin da suka yi murabus akwai Kwamishinan Matasa da Wasanni, Mustapha Rabi’u Kwankwaso; Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dr. Yusuf Ibrahim Kofarmata; Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Nasiru Sule Garo; Kwamishinan Jin Ƙai, Adamu Aliyu Kibiya; da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida, AVM Ibrahim Umar (mai ritaya).
Sauran manyan jami’an da suka yi murabus sun haɗa da Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Kano, Laminu Rabi’u Ɗanbaffa; Shugaban Gidan Zoo na Kano, Sadiq Kura Muhammad; Shugaban Hukumar KARMA, Alhaji Hassan Danbappa; da Sani Shehu Makarya (Igwe China), mai bai wa gwamna shawara kan kasuwar GSM.
Haka kuma, a jerin akwai Walidin Kwankwasiyya, Mai Taimaka wa Gwamna kan harkokin Masarautu; Hajiya A’in Jafaru Fagge, Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Yaɗa Kyakkyawan Saƙo; Mujtaba Muhammad Auwal, Jami’in Alhazai na Karamar Hukumar Gwale; Hon. Nafiu Umar Dankura, Mai Bai wa Gwamna Shawara kan ladabi da tsare-tsare (SSA Protocol) a Abuja; Aminu Sa’idu Meenan Kwankwasiyya; da Shafa’atu Ahmed LondonBe.
A cikin bayanan murabus ɗinsu, jami’an sun bayyana cewa sauye-sauyen siyasa da rikicin cikin gida a jihar Kano ne suka sa suka ɗauki wannan mataki, tare da tabbatar da ci gaba da mara wa tafiyar Kwankwasiyya da jagoranta, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, baya.
Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya koma jam’iyyar APC a hukumance, a ranar Litinin, 26 ga Janairu, 2026.
