News
Gwamnatin Tarayya Na Shirin Bai Wa Polytechnics Damar Fara Bayar Da Shaidar Digiri
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce tana shirin bai wa manyan makarantun kimiyya da fasaha, wato Polytechnics, damar bayar da shaidar digiri, domin kawo sauyi a tsarin ilimi na ƙasar.
Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin wani taron bita da ya haɗa kwamishinonin ilimi na jihohi, shugabannin Makarantu da sauran manyan jami’an ilimi.
ZARGIN YUNƘURIN KIFAR DA GWAMNATI: Falana Ya Bukaci Sojoji Su Ba ’Yan Najeriya Haƙuri
A cewar ministan, gyaran dokar Polytechnics da ake yi a halin yanzu zai magance matsalar banbancin HND da digiri, wadda ta daɗe tana janyo ƙorafi daga masu karatun makarantun fasaha.
Dokta Alausa ya ce wannan mataki wani muhimmin sauyi ne a manufofin ilimi, wanda zai kawo ƙarshen shekaru da dama na nuna wariya ga masu takardun Polytechnics.
Ya ƙara da cewa sauyin ba zai rage ƙwarewar koyarwar aikace-aikace da Polytechnics ke da ita ba, illa ma zai ƙarfafa su tare da ɗaga matsayin shaidar karatun da suke bayarwa.
A cewarsa, ba wa Polytechnics damar bayar da digiri zai ƙara jawo haɗin gwiwa da masana’antu, da kuma ƙara amincewar jama’a da tsarin karatun su.
