News
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mutane Huɗu, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi Masu Yawa A Kano
Rundunar Ƴansandan Jihar Kano ta ce ta samu gagarumar nasara a ƙoƙarinta na yaƙi da safarar da kuma shan miyagun ƙwayoyi, bayan cafke mutane huɗu tare da ƙwato adadi mai yawa na ganyayyakin da ake zargin Cannabis Sativa ne, a wasu samame da aka gudanar a sassa daban-daban na jihar.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar Ƴansandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar 27 ga Janairu, 2026, ya bayyana cewa nasarar ta samo asali ne daga umarni da shawarwarin Sufeto Janar na Ƴansandan Najeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, kan ƙara sintiri da amfani da bayanan sirri domin dakile laifuka.
Gwamnatin Tarayya Na Shirin Bai Wa Polytechnics Damar Fara Bayar Da Shaidar Digiri
Sanarwar ta ce, a ranar 25 ga Janairu, 2026, da misalin ƙarfe 3:00 na rana, jami’an Ƴansanda daga ofishin Fagge, yayin sintirin leƙen asiri a yankin Shataletalen Triumph, sun tare wani Adaidaita Sahu ɗauke da buhuna guda biyu da ake zargi.
Bayan gudanar da bincike, jami’an sun ƙwato kunshin 157 na busassun ganye da ake zargin tabar wiwi ce.
Rundunar ta ce an cafke Amadu Ado da Salisu Lurwanu, dukansu mazauna ƙauyen Kulliya da ke ƙaramar hukumar Bunkure, bisa zargin alaƙa da safarar kayan.
Haka kuma, a wani samame dabam da aka gudanar a ranar 24 ga Janairu, 2026, da misalin ƙarfe 5:25 na yamma, Rukunin Gaggawa na Ƴansanda (RRT), ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ƴansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, sun kai farmaki wasu wurare da ake zargi da aikata laifuka a cikin birnin Kano.
A yayin samamen, jami’an sun cafke Usman Hamisu mai shekaru 22, da Auwal Abdullahi mai shekaru 25. An same su da ganyayyaki 40 da ake zargin tabar wiwi ce, kwalabe 20 na roba solutions, rabin nadi na busassun ganye da ake zargin tabar wiwi ce, da kuma ƙananan kwalabe 10 na wani abu da ake kira da sukudayen.
Ƴansandan sun tabbatar da cewa duk mutanen da aka cafke suna hannunsu, yayin da ake ci gaba da bincike domin gurfanar da su gaban kotu bisa tanadin doka.
A yayin yabawa jami’an da suka gudanar da samamen, CP Ibrahim Adamu Bakori ya buƙaci al’ummar jihar Kano da su kasance masu sa ido, tare da kai rahoton duk wani motsi ko aiki da suke zargi ga ofishin Ƴansanda mafi kusa, domin haɗa kai wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar.
