News
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Nuna Alhini Kan Rasuwar Mutane 30 A Hatsarin Mota A Kano
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana matuƙar alhini kan rasuwar aƙalla mutane 30 da suka mutu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Kwanar Barde, da ke ƙaramar hukumar Gezawa.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi, gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin abin tausayi da babban rashi, ba ga iyalan mamatan kaɗai ba, har ma ga dukkan al’ummar Jihar Kano.
Ja’oji, kungiyar “City Boy Movement” da Samun Nasarar Tinubu
Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya auku ne lokacin da wata tirela da ke kan hanyar Gujungu, wadda ake zargin direbanta da tuƙi cikin ganganci, ta yi taho mu gama da wata motar fasinjoji.
An tabbatar da mutuwar mutane fiye da 30, yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka, kuma ana ci gaba da ba su kulawar lafiya a asibitoci daban-daban a faɗin jihar.
Gwamna Yusuf ya yi addu’ar Allah Ya jikan waɗanda suka rasu, tare da roƙon Allah Ya bai wa iyalansu haƙurin jure wannan babban rashi. Haka kuma, ya yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi cikin gaggawa.
Haka nan, gwamnan ya umarci Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano da ta tabbatar da cewa duk waɗanda hatsarin ya shafa ana ba su cikakken magani kyauta, ba tare da wani jinkiri ba.
