Connect with us

News

Yan Ta’adda Sun Sace Jariri Dan Wata 7 A Borno

Published

on

yan bindiga sun sace mutane

Tsoro da fargaba sun mamaye wasu iyalai a Jihar Borno bayan sace matafiya 13, ciki har da mata da jariri mai watanni bakwai, da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka yi awon gaba da su a kan babbar hanyar Biu zuwa Damaturu gab da kauyen Kamuya cikin jihar Borno.

A rahoton da ya fito na nuna cewa an sace wadanda abin ya shafa tun a ranar 15 ga Afrilu, 2026, lokacin da ‘yan ta’adda suka tare motoci biyu na Golf Wagon da ke dauke da fasinjoji a kan hanya suka tafi da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Advertisement

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Matashin Da Ya Hallaka Mahaifinsa

Iyalan matafiya da aka sace yanzu sun yi kira ga gwamnatin tarayya, gwamnatin Jihar Borno, hukumomin tsaro da sauran hukumomin da abin ya shafa da su kara himma wajen ceto ‘yan uwansu da kuma sake hada su da iyalansu.

Advertisement

An shigar da wannan roko ne a cikin wata sanarwa da Mallam Hassan Yati wani daga cikin jagororinsu ya sanya wa hannu a ranar Laraba a madadin iyalan da abin ya shafa.

A cewar sanarwar, dangin wadanda abin ya shafa sun ci gaba da shiga cikin mawuyacin hali, tsoro da rashin tabbas tun bayan faruwar lamarin, ba tare da wani bayani game da inda ko halin da wadanda aka sace suke ba.

Advertisement

Yati ya koka da cewa, daga cikin wadanda abin ya shafa akwai mata da yara, ciki har da jariri mai watanni bakwai, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin tausayi da kuma tayar da hankali.

Ya ce iyalan sun ci gaba da jure rashin barci, da kuma qaruwar damuwa yayin da kwanaki suka koma makonni ba tare da wani bayani mai ma’ana game da kokarin ceto su ba.

Advertisement

“Iyalan suna kira ga hukumomin gwamnati, hukumomin tsaro, kungiyoyin agaji da duk masu ruwa da tsaki da su gaggauta shiga tsakani tare da tabbatar da ceto matafiyan da aka sace cikin aminci,” in ji shi.

Ya kara da cewa, kowace rana da ke shudewa tana kara wa iyalan da ba su ji ba ba su gani ba wadanda burinsu kawai shi ne ganin ‘yan uwansu sun dawo gida lafiya shiga cikin halin damuwa.

Advertisement

 

 

Advertisement

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending