News
Tinubu, Shettima Za Su Ziyarci Kano Domin Halartar Tarɓar Gwamna Abba Kabir Yusuf Zuwa Jam’iyyar APC
Ana sa ran Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima za su ziyarci jihar Kano domin halartar babbar tarba da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta shirya wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, bayan sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnoni da manyan jiga-jigan APC daga sassa daban-daban na ƙasar za su halarci taron, wanda ake kallonsa a matsayin muhimmin lamari a siyasar Kano da ma Najeriya baki ɗaya.
Gobara Ta Kone Shaguna 85 A Kasuwar Yan Katako Da Ke Rijiyar Lemo A Kano
An tsara gudanar da taron ne ranar Litinin, 16 ga Fabrairu, 2026, a Filin Wasanni na Sani Abacha da ke Kofar Mata a birnin Kano. Masu shirya taron sun ce ana sa ran dubban magoya baya da ‘yan siyasa za su hallara.
Wata majiya a jam’iyyar APC ta bayyana taron a matsayin babban mataki ga jam’iyyar a Kano, wadda ake kallonta a matsayin jiha mai tasiri a taswirar siyasar Najeriya. Ta ce taron zai zama wata dama ta nuna ƙarfi da haɗin kai, musamman a yankin Arewa.
An kafa kwamitoci don shirya taron
Masu shirya taron sun ce sun kafa kwamitoci daban-daban domin tabbatar da gudanar da shi cikin tsari, ciki har da kwamitocin tsaro, lafiya da tsabtace muhalli, kula da wurin taro, yaɗa labarai, tsari da ladabi, da kuma wayar da kai da tattara jama’a.
Masu lura da al’amuran siyasa na ganin taron na daga cikin manyan abubuwan da za su ja hankali a Kano a shekarar 2026, duba da irin manyan jiga-jigan da ake sa ran za su halarta.
