Connect with us

News

Dakarun Sojin Sun Ceto Mutane 8 Da Aka Sace A Yayin Wani Bikin Aure A Kano 

Published

on

‎Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya Da Take Rike Da Su Na Tsawon Kwanaki 10

Dakarun rundunar Brigedeya ta 3 na Sojojin Nijeriya sun samu nasarar ceto mutane takwas daga cikin goma da wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne suka sace a wurin wani bikin aure a Dabawa, ƙaramar hukumar Shanono ta Jihar Kano.

Majiyoyi daga shalkwatar soji sun bayyana cewa maharan, waɗanda ake zargin sun sanya kayan sojoji domin ɓoye ainihinsu, sun kai hari ne ba zato ba tsammani, inda suka yi awon gaba da wasu daga cikin mahalarta bikin.

Advertisement

Tinubu, Shettima Za Su Ziyarci Kano Domin Halartar  Tarɓar Gwamna Abba Kabir Yusuf Zuwa Jam’iyyar APC

Rahotanni sun ce dakarun da ke sintiri a bakin Kogin Yankwada sun garzaya kai ɗauki bayan samun rahoton harin, inda suka bi sawun maharan tare da yin artabu da su a ƙauyen Garu da ke maƙwabciyar Jihar Katsina.

Advertisement

Sojojin sun ci gaba da bin sahun maharan har zuwa kan titin Katsina–Gidan Mutum Ɗaya kafin daga bisani aka rasa inda suka nufa. Sai dai a yayin farmakin, an samu nasarar ceto ’yan mata takwas daga cikin waɗanda aka sace, kuma tuni aka miƙa su ga iyalansu.

Majiyar ta ce ana ci gaba da sintiri da bincike a yankin domin gano sauran mutane biyun da har yanzu ba a ceto su ba, tare da ɗaukar matakan tsaro don hana sake faruwar irin wannan hari.

Advertisement

 

 

Advertisement

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending