Connect with us

News

Kotu ta ɗaure wasu ’yan ƙasar China Shekaru  46 Gidan Gyaran Hali Saboda Damfarar ’Yan Najeriya

Published

on

Babbar Kotun Tarayya da ke Legas a ranar Laraba ta yanke wa wasu ’yan ƙasar China su biyu hukuncin shekaru 46 kowannen su saboda rawar da suka taka a damfarar intanet ta biliyoyin Nairori.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Daniel Osiagor, ya ba su zabin biyan tarar Naira miliyan 56.

Advertisement

Dakarun Sojin Sun Ceto Mutane 8 Da Aka Sace A Yayin Wani Bikin Aure A Kano 

Haka kuma ya umarce su da yin aikin al’umma na tsawon kwanaki uku sannan ya ba da umarnin a mayar da su ƙasarsu ta China idan suka kammala zaman gidan yarin da aikin al’ummar.

Advertisement

Su biyun na cikin mutane 792 da ake zargin da damfara ta intanet da kuɗin kirifto da jami’an Hukumar EFCC suka kama a Legas a watan Disamba 2024.

Sai dai wanda ake tuhuma na uku, Audu Friday, ya ce bai aikata laifi ba, kuma zai ci gaba da fuskantar shari’a.

Advertisement

A zaman kotun na ranar Laraba, lauyar su, Bridget Omateno, ta sanar da kotu cewa Huang da An sun yanke shawarar sauya jawabinsu daga “ba su aikata laifi ba” zuwa “sun aikata laifi.”

“Na farko da na uku sun yanke shawarar sauya jawabinsu. Muna roƙon kotu ta sake karanta tuhumar a kansu,” in ji ta.

Advertisement

Kodayake ba a cimma yarjejeniyar rage hukunci ba, kotu ta amince da buƙatar. Bayan sake karanta tuhumar, Huang da An sun amsa laifi, yayin da Friday ya ci gaba da musantawa.

Mai gabatar da ƙara ta EFCC, Bilkisu Bala-Buhari, ta roƙi kotu ta yanke musu hukunci bisa amsa laifin da suka yi.

Advertisement

A hukuncinsa, Mai shari’a Osiagor ya yanke wa kowannensu hukuncin shekaru 46 a gidan yari, tare da zabin biyan tarar Naira miliyan 56.

Kotu ta kuma amince da buƙatar gwamnati ta kwace dukiyar da aka gano a hannun su yayin bincike.

Advertisement

Abubuwan da aka kwace sun haɗa da: wayoyin hannu 1,596, kujerun ofis 2,120, teburan ofis 544, na’urorin shiga intanet 194, kwamfutoci 43, ƙundun sadarwa, na’urorin sanyaya iska 126, janareto, motoci, gadon katifa da bunkuna da yawa, dubban layukan waya daban-daban, da sauran kayan lantarki da na gida.

 

Advertisement

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending