News
Gidauniyar Bukola Saraki Za Ta Fara Raba Abincin Buɗe Baki Daga Gobe
Gidauniyar Dr. Abubakar Bukola Saraki za ta fara raba dafaffen abinci ga masu azumi a lokacin shan ruwa wanda ta saba yi duk shekara a jihohi bakwai da babban birnin tarayya Abuja.
Rabon abincin wanda ake yi a kwanaki goma na ƙarshe na watan azumin Ramadan yana cikin ayyukan da gidauniyar take yi na tallafawa marasa a ƙarfi a cikin al’umma.
Jami’an NDLEA Sun Kama Wani Tsohon Kansila Da Kilo 40 Na Tabar Wiwi
Wannan shirin wanda aka jima ana yi, yana ɗaya daga cikin shirye-shiryen da gidauniyar take yi a duk lokacin azumi domin tallafawa marasa ƙarfi musamman masu yin azumi tare kuma da tabbatar da ganin cewa al’umma suna buɗa baki da abinci mai gina jiki.
Ciyarwar wannan shekarar za ta gudana ne a jihohin Neja da Sokoto da Bauchi da Borno da Kaduna da Plateau da babban birnin tarayya Abuja, inda ake raba abinci dafaffe a masallatai guda biyu a kowace jiha kuma mutane 100 ne suke amfana da abincin a kullum a kowane masallaci.
A jihar Kwara, inda gidauniyar ta daɗe tana raba abincin a gaba ɗaya faɗin jihar za a raba abincin ne a masallatai daban-daban har guda 52.
Da yake magana gabanin fara rabon abincin, babban daraktan gidauniyar, Dr. Audu Idowu Musa ya ce watan azumi yana bawa masu hannu da shuni dama domin su taimaki mutane tare da sake samun kusanci ga al’umma.
“A irin wannan lokacin al’umma suna tsananin buƙatar taimako musamman magidanta, saboda halin da tattalin arzikin ƙasa yake ciki, samun abinci yana da wahala sosai kuma kowa yana ji a jikinsa ‘ in ji Dr. Audu
Ya ci gaba da cewa “mutane musamman masu ƙaramin ƙarfi suna buƙatar agaji. Saboda haka wannan lokacin shi ne lokacin da ya kamata a taimaki al’umma. Bugu da ƙari taimakawa mutane yana nuna cewa har yanzu akwai mutanen da suka damu da halin da marasa ƙarfi suke ciki a wannan lokacin da rayuwa ta yi tsada.’
Ya ƙara da cewa ciyarwa a cikin azumi ya nuna irin yadda gidauniyar ta saka walwalar al’umma a gaba musamman masu rauni. Shekara da shekaru gidauniyar Abubakar Bukola Saraki tana ayyukan jinƙai, tallafin karatu da lafiya da ci gaban al’umma, kuma wannan ciyarwar tana ɗaya daga ciki.
Gidauniya ta ce waɗanda za su taimaka wajen gudanar da raba abincin da shugabannin al’umma da limamai tuni sun gama shiri wajen ganin komai ya tafi yadda aka tsara.
Gidauniyar ta kuma yi kira ga al’umma da su yi amfani da wannan watan wajen yin addu’ar zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a Najeriya.
