Connect with us

Business

Tashin Farashin Man Fetur Da A Ka Samu A Gidaje Mai, Ya Samo Asali Ne Bisa Yadda Kasuwa Ke Tafiya A Halin Yanzu —NMDPRA

Published

on

FB IMG 1773006543246

Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Najeriya NMDPRA ta bayyana cewa tashin farashin man fetur da a ka samu a gidaje mai, ya samo asali ne bisa yadda kasuwa ke tafiya a halin yanzu.

Mai magana da yawun hukumar George Ene-Ita ne, ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillacin Labarai na Ƙasa NAN a birnin tarayya Abuja, ya yin da yake mayar da martani kan karin farashin man fetur da a ka samu a baya-bayan nan da ke da nasaba da yakin gabas ta Tsakiya.

Advertisement

Gidauniyar Bukola Saraki Za Ta Fara Raba Abincin Buɗe Baki Daga Gobe 

Rahotanni sun bayyana cewa da yawa daga cikin masu ababen hawa a Abuja sun nuna damuwa kan yadda a ka samu hauhawar farashin man, da a baya a ke sayarwa tsakanin Naira 875 zuwa Naira 880 a kan kowace lita.

Advertisement

 

halin yanzu dai ‘yan kasuwa masu zaman kansu na sayar da man tsakanin Naira 960 zuwa Naira 1,000 kan kowace lita zuwa sama, ya yin da su ma gidajen mai mallakin kamfanin mai na ƙasa NNPCL ke siyarwa kusan naira 960 zuwa kan kowace lita.

Advertisement

Kakakin hukumar ya ce bambancin farashin da a ke samu a fadin ƙasar nan ba shi da alaƙa da gwamnati, sai don yanayin kasuwa.

Acewarsa Kasar na amfani da tsarin sayar da man fetur ta hanyar bai’wa kasuwa ’yancin gashin kai, yana mai cewa sauyin farashin na faruwa ne sakamakon yadda kasuwa ke tafiya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending