News
Shugaba Tinubu Bai Da Shirin Sauya Sunan Najeriya Da Soke Shari’a A Arewa —Fadar shugaban kasa
Fadar shugaban ƙasa ta yi fatali da rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na shirin sauya sunan Najeriya zuwa “United States of Nigeria” tare da soke tsarin Shari’a a jihohin Arewa.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 21 ga Mayu, 2026.
Matashiya Mai Koyon Tuƙi Ta Murƙushe Yara Uku ’Yan Gida Ɗaya
Ya bayyana rahotannin a matsayin ƙarya tsagwaronta, yana mai zargin wasu ‘yan siyasa da yada su domin tayar da hankalin jama’a da haddasa rikici gabanin babban zaɓen 2027.
Sanarwar ta ce babu wani shiri da gwamnatin tarayya ke yi na gabatar da wata doka mai suna “Project True Federation” a gaban majalisar dokoki domin sauya tsarin ƙasar kafin zaɓe mai zuwa.
Fadar shugaban ƙasar ta kuma jaddada cewa duk wani yunƙurin sauya kundin tsarin mulkin ƙasa yana buƙatar bin matakai masu tsauri, ciki har da samun amincewar kashi biyu bisa uku na majalisar tarayya da kuma goyon bayan akalla majalisun dokokin jihohi 24.
Ta ƙara da cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na mayar da hankali ne kan aiwatar da gyaran tattalin arziki da samar da ci gaba ga al’umma, maimakon shiga batutuwan da za su haddasa rarrabuwar kawuna a ƙasar.
