News
Yau Shekaru 12 Da Rasuwar Sarkin Kano, Marigayi Ado Bayero
Alhaji Dr. Ado Abdullahi Bayero (1930–2014), Sarkin Kano na 13 kuma mafi dadewa a tarihin masarautar Kano, ya kasance ɗaya daga cikin manyan sarakunan gargajiya da suka yi tasiri a Najeriya da nahiyar Afirka baki ɗaya.
A ranar 22 ga Oktoban 1963 ne ya hau karagar mulkin Kano yana da shekaru 33 a duniya, inda ya yi mulki sama da shekaru 50 har zuwa rasuwarsa a ranar 6 ga Yunin 2014.
Rundunar ‘Yan Sandan Kano Tayi Barazanar Kama Masu Amfani Da Talalmin Taya Akan Tituna
An haifi Sarkin ne a gidan sarautar Fulani Sullubawa, kasancewarsa ɗan marigayi Sarkin Kano, Alhaji Abdullahi Bayero. Kafin hawansa karagar mulki, ya yi ayyuka daban-daban da suka haɗa da ma’aikacin banki a ‘Bank of British West Africa’, ɗan majalisar yankin Arewacin Najeriya, Wakilin Doka na hukumar mulkin gargajiya ta Kano da kuma jakadan Najeriya a ƙasar Senegal.
Marigayi Ado Bayero ya yi fice wajen haɗa kan al’umma, inda ya kasance abin koyi wajen zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabambantan kabilu da addinai. A lokacin Yaƙin Basasar Najeriya, an yaba masa kan rawar da ya taka wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan kabilar Igbo da suka nemi mafaka a Kano.
A bangaren al’adu kuwa, ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa bikin hawan sallah na Kano, wanda ya zama ɗaya daga cikin manyan abubuwan yawon buɗe ido da al’adun gargajiya a Arewacin Najeriya.
Haka kuma ya kasance jagora a harkokin addinin musulunci, mai goyon bayan ilimin addini da na zamani, tare da kasancewa ɗaya daga cikin manyan jagororin darikar Tijjaniyya a Najeriya.
Duk da ƙalubalen tsaro da ya fuskanta, ciki har da harin da aka taba ayarinsa a shekarar 2013, marigayi sarkin ya ci gaba da jagoranci cikin jajircewa. Harin ya yi sanadin mutuwar direbansa da mai tsaronsa, yayin da wasu daga cikin ’ya’yansa suka samu raunuka.
A ranar 6 ga Yunin 2014 ne Allah Ya yi wa sarkin rasuwa a fadarsa ta Gidan Rumfa yana da shekaru 83. Jana’izarsa ta samu halartar dubban jama’a da manyan baki daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje.
Marigayi Ado Bayero ya bar manyan ’ya’ya da suka taka muhimmiyar rawa a harkokin mulkin gargajiya dama gwamnati, ciki har da Alhaji Sanusi Ado Bayero, Alhaji Aminu Ado Bayero wanda daga baya ya zama Sarkin Kano na 15, da kuma Alhaji Nasiru Ado Bayero wanda ya taba zama sarkin Bichi.
A yau shekaru bayan rasuwarsa, ana ci gaba da tuna Marigayi sarkin Kano Ado Bayero a matsayin ɗaya daga cikin fitattun sarakunan gargajiya da suka yi tasiri wajen zaman lafiya, ci gaban ilimi, bunƙasa al’adu da haɗin kan Najeriya.
