News
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ayyana Mataimakin Gwamnan jihar, Murtala Sule Galadima Garo, a matsayin wanda zai yi masa takarar mataimakin gwamna a zaɓen shekarar 2027.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin.
Gwamnatin Legas Ta Kwace Baburan Okada Sama Da 300
A cewar sanarwar, Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawar siyasa da masu riƙe da muƙaman gwamnatin tarayya daga Jihar Kano, waɗanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa. Taron ya gudana ne a masaukin gwamnatin Kano da ke Abuja.
Gwamnan ya ce ya yanke wannan hukunci ne bisa la’akari da irin biyayya, jajircewa da sadaukarwar da Garo ya nuna tun bayan da ya zama mataimakin gwamna, tare da irin gudummawar da yake bayarwa wajen tafiyar da harkokin gwamnati da bunƙasa ci gaban jihar.
Ya ce dangantakar aiki da ke tsakaninsu ta kasance mai ƙarfi, inda ya yabawa mataimakin gwamnan kan ƙwarewa, riƙon amana da kuma yadda yake sauke nauyin da aka ɗora masa.
“Ban taɓa nadamar zaɓen Garo a matsayin mataimakina ba. Ya tabbatar da cewa shi ne ya dace da wannan muƙami, kuma ina da cikakken yaƙini da ƙwarewarsa da irin gudummawar da yake bayarwa ga gwamnatinmu,” in ji Gwamna Yusuf.
-
News6 days ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News7 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mahaifin Prince Adeyemi Adeniyi, Mutumin Da Ake Zargi Da Kafa Hukumar Bogi
