News
Gwamnatin Kano Ta Musanta Rahoton Alƙaluma Kan Yawan Jama’a, Masana’antu da Masallatai
Hukumar Ƙididdiga ta Jihar Kano (KSBS) ta musanta wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta da wasu shafukan intanet, wanda ya ƙunshi alkaluma kan yawan al’ummar jihar, masana’antu, masallatai, coci-coci da kuma adadin yara marasa iyaye da ake zargin suna yawo a titunan Kano.
A cikin wata sanarwa da Darakta Janar na hukumar, Dakta Suraj Sulaiman, ya fitar, ya bayyana cewa rahoton da aka danganta da wani Garba Adamu, wanda wani shafin yanar gizo mai suna The Sultan of Hausa-Land ya wallafa, ba ya ɗauke da sahihan bayanan da Hukumar Ƙididdiga ta Jihar Kano ta fitar.
Hukumar ta ce rahoton ya yi amfani da alkaluma marasa inganci, tare da bayyana cewa adadin masana’antun da ke aiki a Jihar Kano, waɗanda suka haɗa da ƙanana, matsakaita da manyan masana’antu, ya kai 3,632, ba 58 kamar yadda rahoton ya bayyana ba.
Haka kuma, KSBS ta ƙaryata ikirarin cewa Kano na da masallatai 435,389, tana mai cewa bayanan hukuma sun nuna akwai masallatan Juma’a 2,333 da aka tantance.
Dangane da ikirarin cewa akwai yara marasa iyaye miliyan 3.67 da ke yawo a titunan Kano, hukumar ta bayyana adadin a matsayin ƙarya, mai cike da ƙarin gishiri kuma ba shi da tushe a sahihan bayanan ƙididdiga.
KSBS ta buƙaci waɗanda suka wallafa ko suka yada rahoton da su gaggauta janye shi tare da bai wa al’umma haƙuri saboda yaɗa bayanan da ba su da inganci.
Hukumar ta sake jaddada cewa ita ce kaɗai cibiyar gwamnati da ke da hurumin tattarawa, tantancewa da fitar da sahihan alkaluman ƙididdiga na Jihar Kano, tare da kira ga jama’a da kafafen yaɗa labarai da su riƙa tantance sahihancin bayanai kafin wallafawa ko yaɗa su.
-
News6 days ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News7 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
-
News7 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mahaifin Prince Adeyemi Adeniyi, Mutumin Da Ake Zargi Da Kafa Hukumar Bogi
