News
Babu Wani Juyin Mulki Da Ya Yi Nasara A Najeriya Ba Tare Da Sa Hannun Fararen Hula Ba — IBB
Tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya), ya ce duk wani juyin mulkin soja da ya yi nasara a tarihin Najeriya ya samu goyon baya ko taimakon fararen hula.
Babangida ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan rediyon Badeggi 90.1 FM da ke Minna, Jihar Neja, yayin da ake shirye-shiryen bikin cikarsa shekaru 85 a ranar Litinin.
Gwamna Kano Abba Kabir Ya Samu Lambar Yabo Kan Ƙwarewa Wajen Gudanar Da Harkokin Tsaro
Ya ce wasu daga cikin attajiran fararen hula sun taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa juyin mulkin soja a lokuta daban-daban, yana mai cewa ba za a iya danganta irin wadannan sauye-sauyen siyasa ga sojoji kadai ba.
“Babu wani juyin mulkin da ya yi nasara a tarihin Najeriya ba tare da sa hannun fararen hula ba,” in ji shi.
Babangida ya kuma yi magana kan juyin mulkin shekarar 1985 da ya kai ga shari’a da kuma kisan abokinsa na kud da kud, Manjo Janar Mamman Vatsa, wanda a lokacin yake rike da mukamin Ministan Babban Birnin Tarayya.
Ya ce da farko bai yarda da rahotannin da suka alakanta Vatsa da yunkurin hambarar da gwamnatinsa ba, saboda sun dade suna abota, tun daga makarantar Bida Middle School, sannan suka shiga aikin soja a shekara guda.
A cewarsa, an kafa kwamitin bincike domin gudanar da bincike kan zargin, inda aka wanke Janar Mohammed Gado Nasko, yayin da aka samu hujjojin da suka alakanta Vatsa da shirin.
Babangida ya ce lamarin ya girgiza shi matuka, amma dokokin soja ba su ba shi damar yin afuwa ba.
Vatsa dai an kashe shi ne ta hanyar harbin bindiga a watan Maris na 1986. Babangida ya ce mutuwarsa ta kasance daya daga cikin abubuwan da suka fi tada masa hankali a rayuwa.
Da yake magana kan halin da Najeriya ke ciki a yanzu, tsohon shugaban kasar ya bukaci ’yan Najeriya da su yi hakuri tare da ci gaba da bai wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu goyon baya, musamman a yayin da ake fuskantar matsalolin tattalin arziki da tsaro.
