News
Za A Kara Wa Shugaba Tinubu Albashi Don Samun Nutsuwar Sauke Hakkin ‘Yan Najeriya
Hukumar Raba Kuɗaɗen Shiga ta Ƙasa (RMAFC) ta ce ta kammala aikin nazarin albashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da na sauran masu riƙe da muƙaman siyasa, na gwamnati da na shari’a.
Shugaban hukumar, Dr. Mohammed Bello Shehu, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da mambobin ƙungiyar editocin labarai ta NGE a Legas, inda ya gabatar da rahoton ayyukan hukumar da ci gabanta daga shekarar 2023 zuwa yanzu.
Kifewar Kwale-kwale Ta Yi Ajalin Manoma Biyar A Neja
Ya ce an kammala bitar albashin, kuma yanzu batun yana gaban hukumomin da abin ya shafa domin ɗaukar matakin da ya dace.
Ya ƙara da cewa bitar albashin masu riƙe da muƙaman zartarwa da na majalisa na kan matakin ƙarshe, inda ake sa ran za a aika da wani ƙudirin doka mai suna Political and Public Office Holders (Salaries and Allowances) Act, 2026 zuwa Majalisar Ƙasa.
