News
Kotu Ta Aike Da Wanda Ake Zargi Da Satar Takalma A Masallaci Gidan Gyaran Hali A Kano
Wata Kotun Majistare mai lamba 53 da ke Norman’s Land a Jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare wani mutum, Muhammad Najib Rimin Kebe, a gidan gyaran hali bisa zargin satar takalman jama’a a masallacin da ke cikin harabar kotunan.
’Yan sanda ne suka gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotun, wadda Mai Shari’a Dayyabu Jamilu Hamza ke jagoranta, kan zarge-zargen kutsen ba bisa ka’ida ba da kuma satar takalma.
Bayan an karanta masa tuhume-tuhumen, kotun ta umarci a tura shi gidan gyaran hali, sannan ta dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga Agusta, 2026.
A cewar bayanan da aka gabatar a gaban kotun, ana zargin wanda ake tuhuma da yawan zuwa masallacin da ke harabar kotunan, inda ake zarginsa da wawushe takalman masu zuwa ibada.
Wasu daga cikin wadanda suka shigar da korafi, ciki har da ma’aikatan kotu, jami’an ’yan sanda, ma’aikatan hukumar gyaran hali da sauran jama’a, sun ce matsalar satar takalma ta dade tana faruwa a masallacin.
Sai dai kotu ce za ta tabbatar da gaskiyar zarge-zargen da ake yi wa wanda ake tuhuma bayan kammala sauraron shari’ar.
