News
KADUNA: Jami’an Ƴansanda Sun Tarwatsa Sansanonin Ƴan Bindiga A Makarfi
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta ce jami’anta sun tarwatsa wasu sansanonin ’yan bindiga a Ƙaramar Hukumar Makarfi ta jihar.
Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya ce an gudanar da samamen ne ranar 29 ga Agusta, 2026, tare da haɗin gwiwar jami’an Sa-kai na Jihar Kaduna da ke Makarfi.
Rikicin Kan N200 Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 3 Da Ƙone-ƙone A Legas
Ya ce jami’an sun kai samamen ne bisa bayanan sirri da suka samu daga mazauna yankin, inda suka farmaki wuraren da ake zargin ’yan bindiga na fakewa a Durum da Danguzuri, har zuwa kan iyakar Jihar Kano.
A cewar Hassan, jami’an sun kuma rusa wasu gine-gine biyu da aka gano cewa ’yan bindigar na amfani da su wajen tsare mutanen da suka yi garkuwa da su a Rugar Mijin Goggo da Unguwar Maryamu da ke Danguzuri.
Ya ce rundunar, tare da jami’an tsaro na sa-kai, na ci gaba da gudanar da sintiri na haɗin gwiwa a yankin domin hana ’yan bindigar sake kafa sansanoni ko komawa ga ayyukansu.
Rundunar ta ce matakan da jami’an tsaro ke ɗauka sun taimaka wajen dawo da zaman lafiya, inda ta tabbatar wa mazauna yankin cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyinsu.
-
News3 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News6 days ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
-
News4 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
