Connect with us

News

“Rikicin ’Yan El-rufai: Bashir Ya Ce Bello Ba Zai Iya Yi Masa Komai Ba”

Published

on

Bashir El Rufai Bello El Rufai 768x600 (1)

Ɗan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, Bashir El-Rufai, ya ce yana kwana da wuƙaƙe da bindigogi, yana mai cewa ɗan uwansa kuma ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Bello El-Rufai, ba zai iya yi masa komai ba.

Bashir ya bayyana hakan ne a wani jerin rubuce-rubuce da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, inda yake sukar ɗan uwansa kan wasu batutuwan siyasa da na iyali. Daga baya ya goge wasu daga cikin rubuce-rubucen, waɗanda tuni suka yaɗu a kafafen sada zumunta.

Shugaba Tinubu Ya Nemi Kotun Amurka Ta Hana FBI Da DEA Fitar Da Bayanansa

A cikin rubuce-rubucen nasa, Bashir ya soki alaƙar siyasar Bello da Gwamnan Kaduna, Uba Sani, yana mai nuna rashin amincewarsa da yadda ɗan uwansa ke gudanar da harkokin siyasarsa a baya-bayan nan.

Bashir ya kuma yi wasu zarge-zarge kan Bello, ciki har da cewa ya fi mayar da hankali kan shan barasa da amfani da hodar iblis maimakon wakiltar al’ummar Kaduna ta Arewa da suka zaɓe shi a Majalisar Wakilai.

Sai dai waɗannan zarge-zarge da Bashir ya yi ba su samu tabbaci daga wata majiya mai zaman kanta ba, yayin da Bello El-Rufai bai fito fili ya mayar da martani kan zarge-zargen ba a lokacin da rahotannin suka bayyana.

Advertisement

Rikicin ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a kafafen sada zumunta, musamman ganin cewa ’yan’uwan biyu ’ya’yan tsohon gwamnan Kaduna ne, kuma lamarin ya sauya daga sabanin siyasa zuwa musayar kalamai masu zafi tsakanin ’yan uwa.

 

 

DAILY TRUST 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending