Connect with us

News

ATIKU: Babu Uba Nagari Da Zai Bar Gida Na Ci Da Wuta Ya Tafi Hutu

Published

on

Tinubu 3 (1)

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki Shugaba Bola Tinubu kan tafiyarsa zuwa Turai domin hutu a lokacin da Najeriya ke fama da matsalar tattalin arziki da rashin tsaro.

Atiku ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta ranar Lahadi, bayan Shugaba Tinubu ya bar Najeriya zuwa Turai domin yin hutun shekara-shekara na tsawon makonni uku.

KADUNA: Jami’an Ƴansanda Sun Tarwatsa Sansanonin Ƴan Bindiga A Makarfi

Ya ce Najeriya na fuskantar matsaloli da suka haɗa da tsadar man fetur, hauhawar farashin kayan abinci, tsadar sufuri da kuma rashin tsaro, don haka bai kamata shugaban ƙasa ya bar ƙasar a irin wannan lokaci ba.

“Ku duba abin da Bola Tinubu ya bari a baya. Farashin man fetur ya wuce ƙarfin talakan Najeriya. Magidanta na rage yawan abincin da suke ci saboda tsada. Farashin sufuri ya sa mutane ba sa iya zuwa garuruwansu,” in ji Atiku.

Ya ƙara da cewa rashin tsaro na ci gaba da haddasa mutuwar ’yan Najeriya a sassa daban-daban, yana mai cewa shugabanci ya haɗa da sanin lokacin da ƙasa ke buƙatar shugaban ya kasance a gida.

Advertisement

“Uba zai iya yin tafiya idan komai yana tafiya daidai. Amma idan rufin gidansa yana ci da wuta kuma iyalinsa na ciki, ba zai ɗauki akwatinsa ya nufi filin jirgin sama ba,” in ji shi.

Sai dai mai taimaka wa shugaban ƙasa, Sunday Dare, ya kare tafiyar Tinubu, yana mai cewa shugaban ya cancanci yin hutu bayan aiki tukuru da ya shafe yana yi. Atiku ya ce ba ya adawa da shugaban ya yi hutu, sai dai yana sukar lokacin da ya zaɓa na tafiyar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending