Connect with us

News

KARFE BIYUN DARE ZULUM YA DIRA ASIBITIN GWAMNATI NA MONGUNO ZAI KARA KASO 30% NA ALBASHI GA LIKITOCI LGs 7

Published

on

Daga Khadija Abdullahi Mahmud.

 

 

 

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai ziyara babban asibitin Monguno da karfe 2 na daren Asabar
Zulum ya amince da karin albashi kashi 30 na likitocin kananan hukumomin Monguno, Ngala, Dikwa, Kukawa, Kala-Balge, Abadam da Banki
Gwamnan Bornon ya yi umarnin samar da karin gidajen ma’aikata a asibitin, samar da tuka-tuka da na’urar wuta mai amfani da hasken rana
Monguno, Borno – Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, yayin da ya kai ziyara babban asibitin a Konguno, ranar Asabar, ya sanar da amincewa da karin kashi 30 cikin dari na albashin likitoci a kananan hukumomi bakwai ba tare da tsammani ba.

Baya ga likitoci, ma’aikatan lafiya, anguwan zoma, masu gwaje-gwaje a dakin bincike, masu hada magunguna da sauran ma’aikatan lafiya na kananan hukumomi bakwai suma za su amfana da karin kashi 30 bisa dari na albashinsu, don karfafasu wajen gudanar da aiki mai nagarta da kula da fannin lafiya yadda ya dace.

Advertisement

Kananan hukumomin: Monguno, Ngala, Dikwa, Kukawa, Kala-Balge Abadam da Banki cikin Bama wanda suke daga cikin wuraren da ‘yan Boko Haram suka tarwatsa a shekarar 2014, ba tare da an zauna ba na kusan shekaru takwas har zuwa rufe sansanin ‘yan gudun hijara da masu neman mafaka aka yi.

Bulaliyar majalisar dattawa, Barr. Muhammad Tahir Monguno ne ya raka Zulum babban asibitin misalin karfe 1:00 dare suna can har zuwa karfe 2:00 dare.

Dr. Solomon Tiza, shugaban jami’an kiwon lafiya ne ya tarbeshi, gami da kewayawa dashi asibitn.

Da farko dai, a watan Janairu, 2022, Zulum ya daga albashin duka likitocin Borno zuwa matakin da gwanatin tarayya ke biya, don kawo karshen matsalar yadda likitocin jihar ke komawa asibitocin gwamnati don samun albashi mai tsoka.

A shekaru ukun da gwamnan ya yi a mulki, ya amince da daukan ma’aikatan lafiya 676 wadanda suka hada da sama da likitoci 40 masu jinya 241, anguwannin zoma da sauransu.

Zulum ya kwana a Monguno, wanda ke arewacin jihar daga ranar Alhamis zuwa ranar Juma’a, don sauraran koken jama’a.

Advertisement

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending