Connect with us

News

Na ci amanar ‘yan Najeriya idan ban tsaya takarar shugaban kasa ba – Osinbajo

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

 

 

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo a jiya Litinin ya ce ya ci amanar kasa idan bai tsaya takarar mukamin shugaba kasa ba a shekarar 2023.

Mista Osinbajo ya furta wadannan kalaman ne yayin ata ziyara da ya kai jihar Ondo, kuma ya gana da gwamnan jihar Rotimi Akeredolu da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC.

Advertisement

Ya kuma ce rike mukamin mukaddashin shugaban kasa da ya yi a wasu lokuta ya ba shi kwarewar da yake bukata domin ya jagoranci Najeriya.

“Mutane na mutuwa a kowace rana, saboda haka zai kasance cin amanar kasa idan na yi ritaya kuma na koma Legas ko Ikenne bayan wa’adin mulkinmu. Ban yi wa kasar nan adalci ba.”

A nasa bangaren, Gwamna Akeredolu ya ce duk da cewa ‘yan deleget na jihar suna son sa kuma suna mutunta shi, ubaniji ne kawai ke bayar a mulki.

Osinbajo ya sanar da aniyarsa ta neman mukamin shugaban Najeriya a ranar 11 ga watan Afrilu, kuma tun ranar yake kai ziyara sassan kasar yana neman goyon bayan ‘yan kasar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending